16 Afirilu 2020 - 04:59
 Libiya : Gwamnatin Tripoli Ta Kwace Manyan Birane Biyu Daga Hannun Haftar

Sojojin na kasar Libya da su ke biyayya ga gwamnatin hadin kan kasa wacce take da matsuguni a birnin Tripoli wacce kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ke goyon baya, ta sanar da kwace birane biyu masu muhimmanci na Sorman da Sabaratha daga mayakan janar Halifa Haftar.

(ABNA24.com) Sojojin na kasar Libya da su ke biyayya ga gwamnatin hadin kan kasa wacce take da matsuguni a birnin Tripoli wacce kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ke goyon baya, ta sanar da kwace birane biyu masu muhimmanci na Sorman da Sabaratha daga mayakan janar Halifa Haftar.

Mai Magana da yawun gwamnatin ta Libya, Muhammad Gnunu ya ce; sojojin kasar suna ci gaba da farautar mayakan janar Halifa Haftar a cikin yankunan da ake yin fada.

Tun a cikin watan Aprilu na shekarar da ta gabata ne dai, Janar Haftar wanda yake samun goyon bayan kasashen masar, Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa, ya shelanta farmakin kwace birnin Tripoli, amma har yanzu bayan shekara guda bai kai ga shiga cikinsa ba.


/129